Wani ɗalibi a makarantar sakandire, mai suna Mike Ogbese, ya lakaɗawa malaminsa, Ezeugo Joseph, dukan tsiya har ya rasu a kan ya zane ƙanwarsa da bulala.

Mike, wanda ya ke aji na 3 a wata makaranta da ke jihar Delta, ya aikata wannan ɗanyen aiki ne bayan da ya zargi malamin da lakaɗawa ƙanwar sa duka da bulala.

Rikicin ya fara ne bayan da Mike ya samu labarin cewa malamin ya yi wa ɗalibarsa, Promise duka, wacce kuma a ka ce kanwar Mike ɗin ce.

An rawaito cewa Mike ɗin ya kasa jurewa bulalar da a ka yi wa ƴar uwar tasa, shime ya bi malamin ya yi masa duka, inda da ga ƙarshe ya ce ga garinku nan.

 

 

Asalin labari (Daily Nigeria Hausa)

Leave a Reply